1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Tasirin Faransa a kasashen da ta mulka

Salissou Boukari Gazali Abdou Tasawa /LMJ
December 22, 2023

Yayin da sojojin Faransa da ta yi wa Nijar mulkin mallaka suka kammala ficewa daga kasar, ofishin jakadancin Faransa a Yamai ya sanar da rufe kofofinsa sakamakon matsalolin da suke fuskanta.

https://p.dw.com/p/4aVDh
Nijar | Yamai | Sojoji | Faransa
Tun dai bayan juyin mulkin na Nijar, sojojin Faransa a kasar suka fara hada komatsansuHoto: ALAIN JOCARD/AFP/Getty Images

Tashin jirgin karshe na dakarun Faransa a Jamhuriyar ta Nijar din da ya kammala kwashe baki daya sojojin, na nufin kawo karshen duk wata alaka ta soji tsakanin Nijar din da tsohuwar uwar giyar tata da ta yi mata mulkin mallaka. Masana dai na ganin wannan ka iya kawo gagarumin koma baya a yaki da ta'addanci a yankin Sahel, musamman kasancewar an samu makamanciyar wannan baraka tsakanin Mali da kuma Faransan da ita ce ta yi wa Bamakon mulkin mallaka. Sai dai yayin da sojojin Faransan ke kammala ficewa baki daya daga Nijar din, ofishin jakadancin Paris a Nijar din  ma ya bayyana ya bayyana cewa ba ya iya gudanar da ayyukansa yadda ya kamata, dangane da haka tilas ya dakatar da ma'aikata da kuma rufe ofishin baki daya.

Nijar | Faransa | Tsami | Alaka | Juyin Mulki
Tuni dai Faransan ta kwashe 'yan kasarta da ke aiki a ofishin jakadancinta na Yamai.Hoto: Sam Mednick/AP Photo/picture alliance

Cikin wata sanarwa da ofishin jakadancin Faransan a Nijar din ya fitar, ya nunar da cewa tun bayan juyin mulkin da sojoji suka yi da kuma matsalolin da ofishin ya fuskanta musamman ranar 30 ga watan Yuli kwanaki shida bayan kifar da gwamnatin suke fuskantar matsi daga hukumomin mulkin sojan. Ana iya cewa dai wannan wani abu ne da kusan ba a taba gani ba tsakanin kasashen biyu, wanda ya yi kamari tun bayan da sojojin da suka kifar da gwamnatin Shugaba Mohamed Bazoum na Jamhuriyar ta Nijar suka soke duk wata yarjejeniya da aka cimma tsakanin kasashen biyu ciki har da ta tsaro.

Nijar | Mohamed Bazoum | Sojoji | Juyin Mulki
Hambararren shugaban kasar Nijar, Mohamed BazoumHoto: Stevens Tomas/ABACA/IMAGO

Sojojin da suka kifar da zababbiyar gwamnatin dimukuradiyya a Nijar din ne dai, suka dauki matakin sallamar sojojin Faransan da ma jakadanta daga kasar. A cewar sojojin jakadan Faransan na yi musu katsalandan a harkokin kasar ne, kuma wasu masu gwagwarmayar kare hakkin dan Adam kamar Dokta Yahaya Badamasi na ganin tilas a fuskanci kalubale sakamakon wannan matsalar. Shi ma dai Sahanine Mahamadou da ke adawa da gwamnatin mulkin sojan ta Nijar, matakan da sojojin ke dauka za su janyo gagarumin koma-baya ga kasar. Babbar ayar tambayar a nan ita ce, ko har ya zuwa wane lokaci ne wannan kiki-kaka da ke tsakanin Nijar da Faransa za ta kawo kashe domin a kai ga hulda ta kasa da kasa mai amfani ba wai ta mai gida da yaronsa ba?